Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya ta ce sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Afrilun 2024.
Gwamna Abba Kabir ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.
Majalisa ta buƙaci gwamnati ta daina bai wa ƙananan hukumomin da aka naɗa wa kantomomi kuɗi.
Jirgin saman sojoji ya yi hatsari a birnin Fatakwal da ke jihar Ribas.
Gwamnatin tarayya za ta tara N585m da za a biya a matsayin tarar wadanda ke daure a gidajen gyaran hali domin rage cunkoso a fadin kasa.
‘Yan ta’adda huɗu na ƙungiyar ISWAP sun mutu yayin da bam ɗin da suka dasa ya tashi da su a ƙauyen San San, karamar hukumar Mobbor ta jihar Borno.
Rundunar ƴan sanda a jihar Taraba ta ce an kashe ‘yan bindiga fiye da 50 da ake zargin su ne ke addabar karamar hukumar Bali ta Jihar.
Kotu ta yi wa mutum biyu ɗaurin rai-da-rai a kan laifin luwaɗi da yara a Jigawa.
Jim kadan bayan tafiyar sojojin da aka girke a garin Maganda da ke Birnin Gwari jihar Kaduna ‘yan bindiga sun kai hari.
Wasu ƴan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan zaɓe na jihar Kogi Farfesa Hale Gabriel Longpet a birnin Lokoja.
Iran ta yi gargadin ‘sakamako mai tsanani’ bayan da aka koma fagen daga a yakin Gaza.
Rahotanni daga Guinea Bissau na cewa an ji ƙarar harbe- harben bindiga sosai a kudancin babban birnin kasar.
Brazil ta tura dakaru iyakarta da Venezuela yayin da ake ƙara samun zaman ɗar-ɗar.
Everton ta ɗaukaka ƙara kan making da aka cire mata mako 10.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp