Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ce gwmnatinsa na gudanar da tsare-tsare da manufofi da nufin samar wa ‘yan ƙasar ci gaba mai ɗorewa.
‘Yan fashi sun fasa bankuna a Benue, sun kashe DPO da ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kashe matarsa a Borno.
Wani yaro ya mutu yayin da wasu mutum uku suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ba da gudumawar gidansa don binciken addinin Musulunci.
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta fara gudanar da bincike bayan sabon kwamishinan da aka naɗa a jihar ya rasu.
Ɗan tsohon gwamnan Kano, Abdul’aziz Abdullahi Ganduje, ya ziyarci Sanata Kwankwaso, a gidansa da ke unguwar Bompai a Kano.
Ana zargin wasu malaman makarantar Al Azhar Academy dake Kofar Bayan Zaria a jihar Kaduna da kisan wani dalibinsu ta hanyar lakada masa duka.
Limamin kirista a jihar Sokoto Bishof Kukah yace Kafa ‘yantacciyar ƙasar Falasɗinu ne kaɗai zai magance rikicin Isra’ila da Hamas.
A karon farko, rukinin motocin farko dauke da kayayyakin agaji daga Masar sun soma shiga Gaza ta iyakar Rafah.
Akalla mutum 100,000 suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a tsakiyar birnin Landan a yau Asabar.
Lauyoyin Mohamed Bazoum sun ce sojojin Nijar sun kitsa labarin cewa yayi kokarin tserewa domin kawai su ci gaba da musguna masa.
An kone fiye da kaji 45,000 a Mozambique.
Tsohon zakakurin Manchester United, Sir Bobby Charlton ya mutu, yana da shekara 86.
EPL: Liverpool ta sami nasara akan Everton da ci 2:0 a wasan yau.
EPL: Manchester City ta sami nasara akan Brighton da ci 2:1 a wasan yau.
EPL: Sheff Utd tayi rashin nasara da ci 2 da 1 a hannun Man Utd
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo