Daga Baba Usman Gama
Majalisar Dattawa ta amince da tiriliyan N28.7 a matsayin kasafin 2024, bayan nazarin rahoton kwamitinta na kasafin kudi.
Mazauna Legas sun bayyana kokensu ga shugaba Tinubu, inda sukayi ta kururuwa “muna jin yunwa” a harshen Yarbanci a lokacin da ayarinsa ke wucewa.
Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ziyarci iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Da alamu yanayin tsadar kujerar hajji ya kawo cikas ga Hukumar Alhazai ta Kasa wurin cike gurbin kujerun da aka ware mata.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika yara 6 daga cikin 7 da ’yan sanda suka kubutar a jihar daga hannun masu safarar kananan yara zuwa Kudancin Najeriya ga iyayensu, ya kuma ba kowannensu kyautar N500,000.
Tsohon dan takarar Shugaban Kasa na LP Peter Obi da Datti Baba Ahmed sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan tsohon Shugaban Majalissar wakilai, Marigayi Ghali Umar Na’Abba.
’Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen wayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 11 a yankin Achimbi da Gumanyi da ke unguwar Kwaku a yankin Kuje a Abuja.
Ƴan sanda sun kuɓutar da malamin jami’ar jihar Nasarawa da aka yi garkuwa da shi.
Nairar Najeriya ta shige sahun gaban kudade marasa daraja a duniya.
Shugaban Kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi wa fursunoni sama da 1,000 afuwa tare albarkacin bikin Kirsimeti.
An tsare wasu limaman coci biyu kan yi wa mai sukar shugaban ƙasa addu’a a ƙasar Nicaragua.
Adadin wadanda suka mutu a harin Rasha kan Ukraine ya zarta 30.
EPL: Chelsea ta sami nasara akan Luton da ci 3:2 a wasan yau.
EPL: Manchester City ta sami nasara akan Sheffield da ci 2:0 a wasan yau.
EPL: Aston Villa ta sami nasara akan Bunley da ci 3:2 a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl