Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Alhamis 23/11/2023 – 08/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da Abdullahi Sule na APC a matsayin gwamnan Jihar Nasarawa.

Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya.

Tsohon gwamnan Filato Mista Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe ta kasa INEC a yau Alhamis.

Boko Haram ta ba mazauna yankunan Borno 8 kwanaki 3 su tashi.

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya karbi bakuncin Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari, a ofishinsa da ke Abuja.

Anjibge jami’an tsaro a filin Mahaha da ke Kano, bayan hana magoya bayan jam’iyar NNPP gudanar da taron addu’a a filin.

Wani sabon bincike ya gano cewa Jihar Legas na tafka asarar Naira tiriliyan hudu duk shekara saboda cunkoson ababen hawa.

Wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP sun yi salloli da addu’o’i na musamman a Kano, inda suka yi fatan samun nasara a Kotun Kolin Najeriya.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya sasanta sojoji da ‘yan sanda a jihar bayan da suka yi wani karamin rikici a ranar Laraba.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Shugabannin jam’iyyar APC a jihar Rivers sun bijirewa umarnin APC NWC ƙarƙashin jagoracin Ganduje.

An samu tashin gobara a babbar kasuwar Oja Tuntun da ke cikin birnin Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Shugaban mulkin sojin Nijar ya kai ziyarar farko kasar waje ta farko a makwabciyarsu Mali inda shugaban kasar Assimi Goïta ya tarbe shi a Bamako.

Yarjejeniyar dakatar da faɗa a Gaza za ta fara aiki daga 10 na safiyar Juma’a.

Yunwa ta kashe mutum 50 a Habasha.

Farashin ɗanyen man fetur ya ƙara faɗuwa a kasuwannin duniya.

An dakatar da Malema da wasu mutum 5 a majalisar dokokin Afrika ta Kudu.

Dan wasan Manchester United Harry Maguire ya ce ya yafe wa dan majalisar Ghana wanda ya zolaye shi, sannan dan wasan ya ce masa sai sun hadu a Old Trafford.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *