Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Alhamis 04/01/2024CE – 22/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

EFCC ta kai samame hedikwatar rukunonin kamfanonin Ɗangote da ke Legas.

Majiyar EFCC ta ce Sadiya Farouq ta ce rashin lafiya ne ya hanata zuwa hukumar a jiya.

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta cafke wani fasto kan damfarar wani mai a harkar hakar ma’adinai a Jihar Kogi.

Dangote ya faɗo daga matsayin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.

Yan bindiga sun kashe mutum 10 a kauyen Kwanar Dutse da ke masarautar Dansadau dake karamar hukumar Maru jihar Zamfara.

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ‘yan fashin daji 10 a jihar Katsina.

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN ta ce babu kanshin gaskiya dangane da rahotanni da ke yawo cewa za a kara kudin man fetur.

Jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya yi alkwarin daukar fansa mai tsanani kan tagwayen hare-haren da suka kashe mutane 84 a kasar.

Ƴan sanda a Brazil na neman fursunoni fiye da 250 da suka ƙi komawa gidan yari bayan da aka basu dama su je bikin kirsimeti da iyalinsu.

Amurka ta ce karar da Afirka ta Kudu ta shigar a ICC kan Isra’ila ƙage ne.

Shugaban Kenya William Ruto na fuskantar caccaka sakamakon barazanar da ya yi na ƙin mutunta umarnin alƙalai da ya kira “masu cin hanci”.

Jadon Sancho zai koma zaman aro a Dortmund.

Kotun Faransa ta daure Youcef Atal dan wasan Nice watanni 8 kan sakon goyon baya ga Gaza.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *