Daga Baba Usman Gama
Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kwarya kwaryar kasafin kudin 2023 da Shugaban Kasa Tinubu ya aike mata na Naira tiriliyan 2.176.
Gwamnatin Najeriya za ta kashe Naira biliyan 7 wajen kwaskwarimar gidan Tinubu da Shetima.
Karancin danyen mai ya hana Matatar Mai ta Dangote fara aiki da aka yi alkawari a watan Oktoba.
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da tsohon Shugaban Kamfanin Samar da Kayan Noma na Kano (KASCO), Bala Muhammad Inuwa bisa zargin almundahana da dukiyar Jihar Naira biliyan 3.2.
Shugaba Tinubu ya miƙa tutocin APC ga ƴan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnonin da ke tafe.
Raunukan da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamrad Joe Ajaero ya ji sun kara girmama fiye da yadda aka yi tsammani.
An rantsar da Natasha a matsayin sanatar Kogi ta Tsakiya.
An yanke wa mai garkuwa da mutane hukuncin rataya a jihar Anambra.
Gwamnan jihar Jigawa zai gina makarantun Almajirai a faɗin jihar.
Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ma’aikatan kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Usman Sahabi.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Joshua Audu Gana na jam’iyyar PDP a mazabar Lavun/Mokwa/Edati a Neja.
Jaruma fim Hadiza Gabon ta maka wani mutumi a gaban kotu saboda zargin bata mata suna ta hanyar yi mata kage.
Saudiyya ta kaddamar da gidauniyar tallafa wa Falasdinawa.
Uganda ta kama jagoran mayakan da suka kashe masu yawon shakatawa a kasarta.
Amnesty ta zargi ‘yan ta’adda a Burkina Faso da aikata laifukan yaki.
Yau shahararren jarumin fina-finan Indiya, Shah Rukh Khan ya cika shekaru 58.
Rodrygo ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2028 a Madrid.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp