Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Talata 31/10/2023 – 16/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya ware wa INEC Naira Biliyan 18 na zabukan Gwamnonin jihohi 3.

Fadar shugaban kasa tace lokaci ya yi da Atiku zai haƙura da neman zama shugaban ƙasa.

Majalisar Zartaswa ta amince ta karin Naira tiriliyan 2.1 a Kasafin Kudin 2023.

Gwamnan jihar Borno Zulum ya ce matuƙar ba a magance Boko Haram da ISWAP ba, zasu iya shafe taswirar Najeriya.

Bayan an shafe kwana da kwanaki Dalar Amurka ta na tashi a kasuwa, yanzu darajar Naira ta fara farfadowa a Najeriya

Ƴan Sanda sunce an ga gawar malamar Jami’ar Minna, a gidanta kwance malemale cikin jini.

A sakamakon abubuwan da ke faruwa a jihar Ribas, gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP sun kira taro.

Sanata Ali Ndume ya ce ko kusa shi ba sa’an shugaban majalisa, Godswill Akpabio ba ne a sanin harkallar majalisar.

Tsohon shugaban karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai, Elder Raymond Washima Erukaa, ya rasu a hannun yan bindiga bayan anbiya kudin fansa.

Tagwayen da aka haifa a hade a jihar Kano sun bar Najeriya domin yi masu tiyasa a kasar Saudiyya.

Gwamnatin Birtaniya ta kori jami’inta bayan ya nemi a tsagaita wuta a yaƙin Isra’ila da Hamas.

Sojojin Sudan sun tsare ƙananan yara a matsayin sojojin rundunar RSF.

Saudiyya ta dauki nauyin raba tagwayen Kano da aka haifa manne da juna.

FIFA ta jajantawa Diaz na Liverpool kan garkuwa da mahaifansa.

Messi ya sake lashe kambun Ballon d’or a karo na 8.

Laliga: Villarreal ta sami nasara akan Granada da ci 3:2 a wasan jiya.

Seria A: Napoli ta sami nasara akan Empoli da ci 3:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *