Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Talata 07/11/2023 – 23/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Kotu ta buƙaci EFCC ta saki Emefiele ko kuma a kaishi kotu.

Sojojin Najeriya sun ce sun kubutar da matar da ta yi yunkurin kashe kanta a tekun Lagos.

Gobara ta kashe mutane a ofishin jakadancin Canada da ke Abuja.

Zaben Gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi: Shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikata su yi aiki da gaskiya.

Peter Obi, ya ce hukuncin Kotun Koli ba shi ne karshen siyasarsa ba.

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta cewa akwai rikici tsakanin ƙabilu a Kagarko.

An tsinci gawar wata dalibar jami’ar Fatakwal (UNIPORT) wacce aka bayyana sunanta da adaeze a dakin kwananta da ke Aluu, karamar hukumar Ikwerre, jihar Rivers.

Yadda Kwamandan Hisba na Kano ya tattauna da masu amfani da Tiktok da Facebook.

Wata mummunar gobara ta tashi a daya daga cikin manyan shagunan da ke sayar da kayan kamfanin Samsung dake Wuse 2 a Abuja.

Hisba Sheikh za ta bude shafi na musamman tare da ’yan TikTok don bibiyar abubuwan da suke wallafawa a shafukansu da sanin ko sun canza halayyarsu bayan tattaunawa da su.

An yanke ƙafar ɗan wasan fim na Najeriya, Mista Ibu.

Sojojin Isra’ila sun kama fitacciyar ƴar gwagwarmayar Falasɗinawa.

Afirka ta Kudu ta janye jakadanta daga Isra’ila.

‘Yan a-waren Kamaru sun kashe akalla mutum 20.

Motoci 30 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza a yau Litinin.

‘Yan ci rani 32,000 ne suka tsallaka tekun Atlantika zuwa Spain a bana.

Ɗan wasan tsakiya a Manchester United da Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, ya ja hankali ƙungiyoyi daga Saudiyya.

EPL: Chelsea ya sami nasara akan Tottenham da ci 4:1 a wasan jiya.

Laliga: Getafe ta sami nasara akan Cadiz da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *