Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Litinin 29/01/2024CE – 17/07/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Sojoji sun kai samame tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama a maboyarsu a dajin Sunke, Gando, Munhaye da kuma dajin Kuyanbana duk a Jihar Zamfara.

Wasu makarantun Sakandare guda 2 a Nawfia ne suka gamu da iftila’in gobara a karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.

Ali Bello ya zama sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kogi daga hawan Mai girma Ahmed Usman Ododo.

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wasu mutane 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Wasu matasa sun lakadawa hadimin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio duka har ya Kai ga mutuwarsa kan rabon kayan Kirsimeti.

Auren Gata : Gwamnatin jihar Kebbi ta aurar da mata 300.

Kungiyar ECOWAS ta ce ba ta da labarin ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinta a hukumance.

Harin jirgi maras matuƙi ya kashe sojojin Amurka uku a Jordan.

Yan Sanda Turkiyya na neman wasu ‘yan bindiga 2 da suka kai hari Cocin Katolika a birnin Santambul har mutum guda ya mutu.

An kama mutum 2 bisa zargi da hannu a kai hari a wani Cocin Istanbul daya daga cikinsu dan kasar Tajikistan ne, yayin da dayan kuma dan kasar Rasha ne.

AFCON: Congo ta cire Masar, bayan an shafe tsawon lokaci ana kai kawo a bugun fenareti.

AFCON: Guinea ta sami nasara akan Equatorial Guinea da ci 1:0 a wasan jiya.

FA Cup: Manchester United ta sami nasara akan Newport da ci 4:2 a wasan jiya.

La Liga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Valencia da ci 2:0 a wasan jiya.

Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Fiorentina da ci 1:0 a wasan jiya.

Bundesliga: Dortmond ta sami nasara akan Bochum da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *