Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Litinin 23/10/2023 – 08/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara yiwa ƙananan ‘yan mata rigakafin ƙwayar cutar HPV mai haddasa kansar mahaifa.

Kotun daukaka kara takori marasa Rinjayen majalisar Dattawa, Sanata Simon Mwadkon da kuma wani dan majalisar duk a jihar Filato.

Wani malamin islamiyya, Malam Umar Tasi’u ya yi gamo da ajalinsa sanadiyyar dukan tsiya da wasu surukansa suka lakada masa a Jihar Neja.

‘Yan bindiga sun buɗe wa ayarin Gwamnan Kogi Yahaya Bello wuta.

An kama wadanda ake zargi da yi wa mai mace ’ya’ya 8 yankan Rago a jihar Gombe.

Gwamnan jihar Kogi ya musanta yunkurin hallaka shi.

Gwamnatin Borno ta haramta bara a Maiduguri.

Dubban mutane a Bosnia sun gudanar da zanga zangar lumana, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

Rundunar sojin Ghana ta ceto mutum 12,000 daga ambaliyar ruwa.

Isra’ila ta kashe ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya 29 a Gaza.

Karin motoci 17 dauke da kayan agaji sun shiga Zirin Gaza ta mashigin Rafaa.

Sojin Masar sun ji rauni a harin da Isra’ila ta kai musu bisa kuskure.

EPL: Aston Villa ta sami nasara akan West Ham da ci 4:1 a wasan jiya.

Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Athletic Club da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Juventus ta sami nasara akan Ac Milan da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *