Daga Baba Usman Gama
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi magabancinsa da neman amfani da matsayinsa wajen canza hukuncin kotun koli ya ce Ganduje ya yi yunkurin ganin an tursasa alkalai a kan zaben jihar Kano.
Akalla fasinjoji 45 ne acikin wasu manyan motocin aka sace a Orokam dake kan hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Ogbadigbo ta jihar Benue.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya sanya Ganduje da Gawuna cikin zauren dattawan Kano.
Hukumar NYSC ta sanar da cewa ta tura wasu matasa 10 zuwa kasar Indiya domin halartar wani shirin musayar matasa da kungiyar Kadet Corps ta Indiya ta shirya.
Kano: Muhammadu Sanusi II ya ce ana karbar kaddara ne bayan zabe ba sai da kotun karshe tayi hukunci ba.
Tsohon Ministan Sadarwa na Zamani, Isa Pantami, ya samo wanda zai biya miliyan 50 daga Naira miliyan 100 na kudin fansar sauran ’yan mata ’yan gida daya da ’yan bindiga suka sace a Abuja.
Mota ta take wani mai kwacen waya a lokacin yake kokarin tserewa bayan ya yi wa wata mata fashin wayarta a titin zoo road dake garin Kano.
An naɗa Frederik na 10 a matsayin sabon Sarkin Denmark.
Mahaƙan zinare fiye da 20 sun mutu saboda zaftarewar ƙasa a Tanzaniya.
Zaftarewar kasa ta hallaka sama da mutane 30 a Columbia.
Super Cup Final: Real Madrid ta sami nasara akan Barcelona da ci 4:1 a wasan jiya.
AFCON: Egypt da Mozambique sun tashi 2:2 a wasan jiya.
AFCON: Cape Verde ta sami nasara akan Ghana a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl