Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Litinin 09/10/2023CE – 24/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya mayar da wani bangare na tallafin kudaden man fetur.

Shugaba Tinubu yace ‘yan Najeriya dubu 500 za su samu guraben aiki a kamfanin sarrafa karfe na Ajaokuta.

Tsohon ministan wasanni Solomon Dalung ya na ganin babu tausayi a tsare tsaren da Bola Tinubu ya kawo.

Ya zuwa yanzu Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya naɗa hadimai kusan 406 waɗanda suke aiki da shi.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a wata ziyarar bazata da ya kai ya gwangwaje marasa lafiya da kyautar Naira 20,000 kowannensu a babban asibitin Sir Sunusi da ke garin Kano.

An cafke jami’in gidan yari kan zargin luwadi da ƙaramin yaro a Gombe.

Wasu yan APC a jihar Kaduna sunyi korafin cewa an mayar da su saniyar ware wajen rabon muƙamai.

Gwamnatin Isra’ila tace an kashe Isra’ilawa sama da 600.

An gudanar da jana’izar mutanen da suka rasu a Zirin Gaza.

Shugaba Erdogan na Turkiyya yace za’a samu zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya ne kawai idan aka samar wa Falasdinawa kasa mai cin gashin kanta.

China ta kira Amurka da ta kasance mai warware rikicin Isra’ila da Hamas a hankali.

Bowen ya rattaba hannu a kwantragin shekaru bakwai da West Ham.

Laliga: Barcelona da Granada sun tashi 2:2 a wasan jiya.

Lig 1: PSG ta sami nasara akan Rennes da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *