Daga Baba Usman Gama
Hukumar Tashoshin Ruwa ta maida wa kamfanin Intels aikin karɓar haraji a tashoshin ruwa.
Ministan yada Labarai yace Gwamnatin Tinubu za ta dawo wa NTA da FRCN da martabar su.
Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sojoji a cikin makon jiya sun kashe ƴan ta’adda 180, sun kama wasu 204 sannan sun ceto mutum 234 da aka yi garkuwa da su.
Ifeanyi Araraume ya ce Bola Tinubu ya sabawa doka da ya nada shugabannin NNPCL a Nuwamba.
Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana cewa za ta kwace duk gidan da babu banɗaki a jihar.
Wani magidanci Yekini a Ibadan jihar Oyo ya roki kotu ta raba shi da matarsa saboda dukan tsiya da ya ke sha hannun ta.
Hukumar Sibil Difens ta kama mutane 42 kan zargin sata, sojan gona da mallakar haramtattun makamai da sauran laifuka a Jihar Borno.
‘Yan sanda sun cafke wani matashi dan shekara 21 bisa zargin yi wa makwabcinsa yankan rago saboda abinci a Jihar Edo.
Wata Kotu dake Eket a jihar Akwa-Ibom ta yanke wa Uduak Moses hukuncin daurin rai da rai bisa laifin yiwa ƴan mata masu shekaru 15 da 14 fyade.
APC ta lashe zaben duk kananan hukumomin Ekiti.
Kungiyar Houthi ta kasar Yemen ta ce ba za ta bari Isra’ila ta sakata ba har sai ta daina kai hari “a kan ‘yan uwanmu da ke Gaza.”
Wazirin Jamus Olaf Scholz ya ce ya kadu da harin da ya hallaka wani dan kasarsa a Paris.
Manchester United za ta iya sayar da Jadon Sancho, da van de Beek, zuwa Juventus kan fam miliyan 26.
Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Atletico Madrid da ci 1:0 a wasan jiya.
Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Napoli da ci 3:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp