Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu, ya naɗa Dakta Musa Adamu Aliyu tsohon kwamishinan shari’ar jigawa a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.
Shugaba Tinubu ya cire shugaban hukumar Alhazai ta kasa, ya nada Jalal Ahmad Arabi sabon shugaban Hukumar.
Majalisar dattawa za ta tantance sabon shugaban hukumar EFCC a yau Laraba.
Mataimakin kwmishinan ƴan sanda a Bayelsa ACP Oluseye Odunmbaku ya mutu yana tsaka da barcinsa.
Majalisar Wakilai ta umarci Gwam atin tarayya ta bude iyakokin ta da Nijar.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta ɗebi tubabbun ‘yan daba aiki.
’Yan sanda a Jihar Oyo sunce mutum 6 sun mutu a wani fada tsakanin manoma da makiyaya a yankin Iwerele na Karamar Hukumar Iwajowa dake Jihar.
Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana rahoton cewa gwamna Rotimi Akeredolu zai koma ƙasar Jamus domin jinya a matsayin wanda babu gaskiya a cikinsa.
Akalla mutum 500 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai kan wani asibiti a Gaza.
Falasɗinawa na arangama da ‘yan sanda a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya soke ganawa da shugaban Amurka Biden.
Shugaban Tarayyar Afirka ya ce harin da Isra’ila ta kai a asibitin Al Ahli da ke Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da Falasdinawa 500, laifin yaki ne.
Jordan ta soke taron da za ta yi da Biden bayan Isra’ila ta kai hari asibitin Gaza.
Shugaban Falasɗinawa ya ayyana makokin kwana uku bayan hari kan asibiti.
Tsohon shugaban Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi yace ya kamata shugabannin Afrika su fitar da jama’ar Nijar daga kunci.
Sojan Nijar 6 sun rasu yayinda suka hallaka ‘yan ta’adda 31 a wani gumurzu a jihar Tilabery.
Dubban mutane ne suka fantsama kan tituna a fadin duniya domin yin zanga-zanga bayan Isra’ila ta kai hari a asibitin Al Ahli da ke Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 500.
Euro Qualify: France ta sami nasara akan Scotland da ci 4:1 a wasan jiya.
Euro Qualify: Ingila ta sami nasara akan Italy da ci 3:1 a wasan jiya.
Uruguay ta sami nasara akan Brazil da ci 2:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo