Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Laraba 06/12/2023C – 23/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Bayan gayyatar su har sau 4 basu zo ba Kwamitin majalisar wakilai kan ƙorafe-ƙorafen jama’a ya bayar da sammacin kama sabon gwamnan CBN, Babban Akanta Janar ta Tarayya, da wasu mutum 17.

Kwankwaso ya jajantawa mutanen Tudun Biri a kan abin da ya faru da su sannan ya koka kan abin da ya faru, yake cewa ba yau sojoji su ka soma hallaka mutanen da ba su yi laifi ba.

Ƙungiyoyin addini sun bukaci a yi bincike mai zurfi kan harin Kaduna.

Mahara sun kashe mutane 33 a wasu kauyuka uku a Karamar Hukuma Bali a Jihar Taraba.

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiya Izalatil Bid’ah ta Kasa, Sheikh Yahya Jingir, ya ce kada Gwamnati ta kawo maganar neman a bar wa Allah kisan da sojoji suka yi wa musulmai a Jihar Kaduna, domin Allah ne Ya yi umarnin a hukumta duk wanda ya aikata irin haka.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya amince da ranar Laraba 27 ga watan Disamba domin biyan ma’aikata albashin wata na 13 a jihar.

Allah yayiwa shugaban karamar hukumar Gombe ta jihar Gwambe rasuwa.

Mazauna Tudun Biri sunce duk da abin da ya faru, sojoji da gwamnati ba su tura jami’ai domin a ceto wadanda aka jikkata ba.

Wata kotu a garin Jos na Jihar Filato ta yanke wa wani matashin hukuncin daurin wata shida kan laifin satar magi da sabulun wanka.

Attahiru Bafarawa ya bukaci sojoji su biya diyya da kuma sauyin matsuguni ga iyalan da harin Mauludin Tudun Biri ya shafa.

Haryanzu al’ummar garin Danjibga dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara suna cikin firgici sakamakon yanda yan bindiga sukayi musu qawanya.

Wani mutum da ke cikin gabatar da jawabi a taron Maulidin Tudun Biri da sojoji suka jefa musu bam ya bayyana yadda ‘ya’yansa da ‘yan uwansa da wasu danginsa suka mutu.

Gobarar daji ta tafka barna a gabashin Nijar.

EPL: Arsenal ta sami nasara akan Luton da ci 4:3 a wasan jiya.

EPL: Wolves ta sami nasara akan Burnley da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *