Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya tace matatar man Kaduna za ta fara aiki gadan gadan a karshen 2024.
Motocin da aka sayowa ‘yan majalisar wakilan tarayya sun fara shigowa hannunsu duk da korafin facaka da ‘yan Najeriya su ke yi.
Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da roƙon da Binani ta yi na hana ci gaba da shari’ar Ari, dakataccen Kwamishinan Zaɓen Adamawa.
Hadiza Bala Usman ta yi raddi ga Rotimi Amaechi da ya daina halin yara na shirga ƙarya.
Ohinoyi: Sarkin Kasar Ebira ya rasu.
Ana zargin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin murɗe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta hanyar naɗa mambobin APC a matsayin RECs na INEC
Al’ummar Musulmi a jihar Oyo sun kafa kwamitin da zai ladabtar da malamai ma su kawo bidi’a cikin addini.
Hukumar makarantar sojoji ta NDA ta fitar da sanarwar dibar dalibai da su ke da sha’awar shiga makarantar a karo na 76.
Gwamnatin Nijeriya ta ce ya kamata a aiwatar da tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra’ila masu cin gashin kansu don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin bangarorin biyu.
Hamas na son a saki fursunoninta da ke Isra’ila kafin ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su.
Erdogan ya ce zai ayyana Isra’ila da mai ‘aikata laifukan yaƙi’.
Rokokin da aka harba daga Gaza sun faɗa kudancin Isra’ila.
Cutar kwalara da zazzabin dengue sun kashe sama da mutum 100 a Sudan.
Dubban magoya bayan Falasdinu ne suka fito zanga-zanga a titunan Landan a mako na uku a jere domin kira a kawo karshen hare-haren Isra’ila a Gaza.
Laliga: Sevilla da Cadiz sun tashi 2:2 a wasan jiya.
Seria A: Juventus ta sami nasara akan Hellas Verona da ci 1:0 a wasan jiya.
NPFL: Enugu Rangers ta Sami nasara akan Kano Pillars da ci 4:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp