Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Lahadi 15/10/2023 30/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Ƙasa da wata 1 bayan sace ɗalibai mata na jami’ar Gusau ƴan bindiga sun sake kai sabon hari a jami’ar miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu ɗalibai biyu na jami’ar.

Gwamnatin tarayya ta nemi aron bashin Dala miliyan 400 daga bankin duniya da nufin a rabawa marasa karfi a kasar nan.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sun shirya tsaf shirin don biyan masu cin gajiyar N-Power bashin da su ke bi na watanni 8.

Hukumar EFCC ta tona yadda aka sace dalolin kudin aikin wutar Mambila aka yi amfani da su wajen sayen gidaje.

Sojoji sun kubutar da mutum 6 da akayi garkuwa dasu a jihar Kaduna, yayin da yan bindigar suka tsere da muggan raunuka a jikinsu.

Sojoji sun kubutar mutane masu yawa da akayi garkuwa dasu a kauyen Igaji a karamar hukumar Ohimini a jihar Benue.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas ta gwamnati da ke dauke da fasinjoji a jihar Benue.

Gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana cewa ba a biya ko sisi a matsayin kuɗin fansa ba kafin a sako ɗaliban jami’ar jihar.

Wata tsohuwa ’yar shekar 72 da wasu mutum biyu sun rasu a sakamakon hatsarin motar fasinja da wata babbar mota a cikin dare a yankin Gbagada da ke Jihar Legas.

Ana zargin wata matar aure da kona dan kishiyarta da dutsen guga kan Naira 200 kacal a jihar Kuros Riba.

Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan a jihar Yobe.

‘Yan sanda sun kama mutane shida a Borno kan zargin satar taragon jirgin kasa.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da kisan Amurkawa 29 a harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila.

Euro Qualifying: Italy ta sami nasara akan Malta da ci 4:0 a wasan jiya.

Euro Qualifying: Germany ta sami nasara akan America da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *