Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Juma’a 27/10/2023 – 12/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa dakarun soji sun kashe ‘yan ta’adda sama da 100 a wani luguden wuta ta sama a iyakar jihohin Zamfara da Neja.

Hatsarin jirgin ruwa ya sa jam’iyyar APC ta dakatar da gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takararta a jihar Bayelsa.

APC ta ce nasarar da Tinubu ya samu a Kotun Koli nasara ce ga dimokuraɗiyya da kuma al`ummar Najeriya.

Dauda Adamu Kahutu yayi taron manema labarai ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta damalamala komai kafin ta bar shugabanci.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda, ya ce gwamnatinsa ba zata nemi tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga ba ta ko wace hanya.

Allah ya yi wa daraktan midiya na kwamitin kamfen jam’iyyar APC a jihar Bayelsa, Mista Terry Tukuwei, rasuwa sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya rutsa da shi.

Majalisar Dattawan Amurka ta ki amincewa a janye dakarun kasar daga Nijar.

‘Yan Isra’ila da Falasɗinawa na fargaba kan mugun abin da zai zo bayan rikicin Gaza.

Shugaban ƙasar Turkiyya ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza.

Shugabannin Turai sun yi kira a dakatar da faɗa don kai kayan agaji Gaza.

Faransa ta ce yawan ‘yan kasarta da aka kashe a harin Hamas sun kai 35.

Rashin iskar Gas ya haifar da katsewar wutar lantarki a Ghana.

Iran na neman ƙulla alaƙa da shugabannin mulkin sojin Nijar.

An samu wata mace da laifin kai wata yarinya ‘yar Birtaniya zuwa Kenya don yi mata kaciya.

Europa: Liverpool ta sami nasara akan Toulouse da ci 5:1 a wasan jiya.

Europa: Brighton ta sami nasara akan Ajax da ci 2:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *