Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Asabar 18/11/2023 – 04/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu zai halarci taron G20 a Jamus ‘don janyo hankalin masu zuba jari’.

Tinubu ya dakatar da yanke kashi 40 na kudin shigar da jami’o’i ke samu.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan yace da Diri bai sake lashe zaɓensa ba, da ya mayar da mahaifiyarsa daga Otueke zuwa Abuja.

Shugaban jami’yyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya sha alwashin yin kaca-kaca da jam’iyyar NNPP a kotun koli.

An jikkata mutane da dama sakamkon wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garuruwan Dusai da ’Yan Gamji na Karamar Hukumar Dambatta a Jihar Kano.

Dakarun Sojin sama sun yi wa ofishin EFCC na Kaduna diran mikiya, suka yi kokarin arcewa da wasu sojoji dake tsare.

Sojoji sun kama mai tsegunta wa ’yan ta’adda bayanansu a Borno.

Gwamna Uzodimma da Diri sun karɓi takardun shaidar cin zabe.

An kama wani ɗan majalisar dattijan Faransa bisa zargin ɗirka wa wata ‘yar majalisa wata ƙwaya da nufin haike mata.

Shugaban Liberia George Weah ya kira abokin hamayyarsa Joseph Boakai ta wayar tarho inda ya amsa shan kaye sannan ya taya shi murna.

Shugaban Amurka Joe Biden na fuskantar ƙaruwar matsin lamba don ya tilasta wa Isra’ila ta dakatar da yaƙin da take yi da Hamas a Gaza.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya soki Ƙasashen Yammacin Duniya kan goyon bayan Isra’ila da suke yi a kashe-kashen da take yi a Gaza.

Ministan Ayyukan Gona na Rasha ya ce sun fara aika hatsi tan 200,000 kyauta zuwa ƙasashen Afirka, kamar yadda Shugaba Putin yayi alkawari a watan Yuli.

Kasashe 5 sun maka Isra’ila a kotun ICC saboda yakin Gaza.

Kotun ECOWAS ta yi watsi da bukatar Sonko na tsayawa takarar shugabancin Senegal.

Babbar kotun Kenya ta haramtawa gwamnati tura ‘yan sanda zuwa Haiti.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

England ta sami Nasara akan Malta da ci 2:0 a wasan jiya.

Columbia ta sami nasara akan Brazil da ci 2:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *