Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 16/12/2023 – 03/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Sowore ya kalubalanci Tinubu ya halarci gasar tseren duniya ta ECOWAS da za a yi a Abuja.

Babban Hafsaon Tsaron Najeriya, ya ce rundunar tsaro za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin da jirgin soji a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Kungiyar MSF ta ce karuwar hare-hare a jihar Zamfara ta tilasta mata janye wasu ma’aikatanta daga garin Zurmi, inda aka yi gumurzu sosai a kusa da asibitin da suke aiki.

Wasu ’yan bindiga sun halaka hakimin garin Sarkin Kudu da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Shugaban kungiyar ta ASUU ya koka kan yadda Tinubu ya saba alkawarin da ya dauka a yayin yakin zabe sannan ya ce 7% kacal gwamnatin tarayya ta ware za a kashewa bangaren ilmi a Najeriya a 2024.

An sako ɗaliban Jami’ar Dutsin Ma dake jihar Katsina da ‘yan fashin daji suka sace.

Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar Ribas sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya ja kunnen Nyesom Wike.

Kansila ya jefa bam a taron ƙaramar hukuma a Ukraine.

Babban kamfanin fiton kayayyaki na ƙasar Denmark, Maersk ya ce zai dakatar da duka ayyukansa a tekun Maliya.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe ‘yan ƙasar uku da Hamas ke garkuwa da su.

Turkiyya ta gina katangar kankare mai tsawon kilomita 170 tsakaninta da Iran.

Sojojin Nijar sun amince su mika mulki ga farar hula.

EPL: Tottenham ta sami nasara akan Nottm Forest da ci 2:0 a wasan jiya.

Seria A: Genoa da Juventus sun tashi 1:1 a wasan jiya.Labaran Safiyar Asabar 16/12/2023CE – 03/06/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Sowore ya kalubalanci Tinubu ya halarci gasar tseren duniya ta ECOWAS da za a yi a Abuja.

Babban Hafsaon Tsaron Najeriya, ya ce rundunar tsaro za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin da jirgin soji a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Kungiyar MSF ta ce karuwar hare-hare a jihar Zamfara ta tilasta mata janye wasu ma’aikatanta daga garin Zurmi, inda aka yi gumurzu sosai a kusa da asibitin da suke aiki.

Wasu ’yan bindiga sun halaka hakimin garin Sarkin Kudu da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Shugaban kungiyar ta ASUU ya koka kan yadda Tinubu ya saba alkawarin da ya dauka a yayin yakin zabe sannan ya ce 7% kacal gwamnatin tarayya ta ware za a kashewa bangaren ilmi a Najeriya a 2024.

An sako ɗaliban Jami’ar Dutsin Ma dake jihar Katsina da ‘yan fashin daji suka sace.

Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar Ribas sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya ja kunnen Nyesom Wike.

Kansila ya jefa bam a taron ƙaramar hukuma a Ukraine.

Babban kamfanin fiton kayayyaki na ƙasar Denmark, Maersk ya ce zai dakatar da duka ayyukansa a tekun Maliya.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe ‘yan ƙasar uku da Hamas ke garkuwa da su.

Turkiyya ta gina katangar kankare mai tsawon kilomita 170 tsakaninta da Iran.

Sojojin Nijar sun amince su mika mulki ga farar hula.

EPL: Tottenham ta sami nasara akan Nottm Forest da ci 2:0 a wasan jiya.

Seria A: Genoa da Juventus sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *