Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Alhamis 12/10/2023CE – 27/03/1445 AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

EFCC ta na binciken tsofaffin gwamnoni, wasu tsofaffin ministoci da jami’an gwamnati da ake zargin sun sace biliyoyi.

Rundunar sojojin saman Najeriya ta sami ƙarin jiragen yaƙi guda 2.

An samu wani likita da safarar sassan jikin mutum a jihar Filato.

An damfari matar Sarkin Bichi Mai martaba Nasir Ado Bayero Hajiya Faridah Nasir Bayero N20m Lamarin ya kai gaban kotu bayan hukumar EFCC ta gurfanar da wanda ake zargin domin a ƙwato mata haƙƙinta.

Mahukunta sun kame gurbatattun kayayyaki na miliyoyin a jihar Neja.

Sama da ƴan bindiga 100 ne suka mutu bayan harin da jiragen yaƙin rundunar sojin sama suka kai a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

ASUU ta yi bore kan sanya jami’o’i masu zaman kansu a tsarin TETFUND.

Dubun wani matashi mai shekara 37 ta cika bayan da ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 62 fyade a Jihar Borno.

Cutar mashaƙon diphtheria ta kashe mutum 20 a Kaduna.

Isra’ila ta tabbatar da mutuwar sojojinta 169 a gumurzu da mayakan Hamas.

Mali ta ce ba ta bai wa Air France izinin ci gaba da zuwa kasar ba.

Ana matsa wa Isra’ila lamba domin ta bari a shigar da kayan agaji zuwa Gaza.

Maguire yace cin zarafin da ake mishi ya fi illa ga ‘yan uwa da iyalansa fiye da shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *