Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Alhamis 07/06/1445 – 21/12/2023

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta tabbatar da mutane 11 da za a naɗa a matsayin alƙalan kotun ƙolin Najeriya.

Rundunar yan sanda ta kai samame wani kamfanin da ake yin jabun lemun kwalba a jihar Lagas.

Yau Alhamis Kotun Kolin za ta yi zama kan shari’ar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kan takaddamar nasarar zaɓensa.

Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da matarsa sun halarci liyafar da aka yi wa sojojin da su ka yi ritaya.

An gurfanar da wasu maza su biyar kan zargin su da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano.

Wani magidanci a Kano ya maka matarsa da mahaifinta a kotu kan zargin su da boye wasu daloli da dansa ya tsinta shekaru biyu da suka gabata.

Mummunan gobara ta lakume shaguna akalla 30 a babbar kasuwar Nkpor da ke jihar Anambra.

Gwamna Umar Bago na jihar Niger ya ba da hutun kwanaki bakwai ga ma’aikatan jihar don su yi bukukuwan Kirsimeti.

Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari garin Chibok da ke a jihar Borno, inda suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

Saurayi ya hallaka budurwarsa a kan 5000 a jihar Bauchi.

Gwamnan jihar Cross River ya amince da hutun kwanaki 14 ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar.

Malaysia ta haramta wa jiragen dakon kaya na Isra’ila shiga tashar ruwanta.

Bankin raya ƙasashen Afirika zai janye gaba daya ma’aikatansa ‘yan ƙasashen waje daga Habasha bayan cin zarafin ma’aikatansa da jami’an tsaron ƙasar suka yi.

Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Almeria da ci 3:2 a wasan jiya.

Bundesliga: Bayern Munich ta sami nasara akan Wolfsburg da ci 2:1 a wasan jiya.

Manchester United na son sayen dan wasan Real Sociedad Takefusa Kubo domin maye gurbin Antony.

EFL: Liverpool ta sami nasara akan West Ham da ci 5:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *