Daga Baba Usman Gama
Fadar shugaban kasa tace takardun karatun Tinubu ba na bogi ba ne.
Atiku zai gudanar da taron manema labarai na kasa da kasa a yau Alhamis.
An sallami ɗan sanda bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 16 fyade a lokacin da take tsare a ofishin ‘yan sanda a jihar Benue.
Ƴan sanda sunce sun kama 1 daga cikin wanda suka kitsa sace ɗaliban Jami’a a Katsina.
Wata kotu a jihar Legas ta yanke wa wanda ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a coci ɗaurin rai da rai.
Gwamnatin jihar Osun ta sanya sabuwar dokar hana fita a ƙananan hukumomin 2 na jihar, biyo bayan rikicin ƙabilanci.
Bankin duniya ya ce ana sa ran bunkasar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar sahara zai ragu a bana, sakamakon faduwar darajar kudi da ake samu a kasashen Afirka ta Kudu, Najeriya da kuma Angola.
Ma’aikatan asibiti sun tsunduma yajin aiki a Amurka.
Masu fafutika sun zargi jami’an tabbatar da da’a na Iran da dukan wata yarinya da ba ta sanya hijabi ba har sai da ta suma.
‘Yan Tawayen Arewacin Mali sun ce sun kwace sansanin Sojoji.
An yanke wa ma’aikacin asibiti a Kenya ɗaurin shekara 35 kan satar yara.
Mutane 21 sun mutu bayan motarsu ta kama da wuta Italiya.
UCL: Newcastle sun sami nasara akan PSG da ci 4:1 a wasan jiya.
UCL: Barcelona sun sami nasara akan FC Porto da ci 1:0 a wasan jiya.
UCL: Manchester City sun sami nasara akan RB Leipzig da ci 3:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
Kano state government has taken the right step in the right direction. I hope other states will do the same.