Daga Baba Usman Gama
Majalisar dokokin jihar Ribas zata tantance shugabannin riko na kananan hukumoni a yau.
Babban lauyan Najeria, Femi Falana, ya tunatar da babbar kotun tarayya da kotun masana’antu ta kasa cewa ba su da hurumin shiga al’amuran da suka shafi sarauta a kasar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta rufe tare da karɓe iko da kananan hukumoni 23 dake jihar.
Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar-Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya da su ci gaba da ƙoƙartawa wajen kakkaɓe ragowar ’yan Boko Haram.
Dandazon magoya bayan ɗarikar Kwankwasiyya sun yi cikar ƙwari a gidan jagoran jami’yyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso domin taya shi murnar bikin sallah babba.
An rasa rayuka bayan ‘yan sanda sun mamaye sakateriyar dukkan ƙananan hukumomin Jihar Ribas.
Jam’iyyar APC ta nemi hukumomin tsaron Najeriya da su gaggauta cafke Kwankwaso.
Allah ya yi wa mahaifiyar Sanata Bukola Saraki rasuwa!.
Mutane sun mutu sakamakon tashin gobara a ‘ma’ajiyar makamai mafi girma’ a Chadi.
Ƴan tawayen FPL sunce su suka kai hari kan bututun man Nijar.
An fara taron baje-kolin makamai mafi girma a duniya, wanda a yanzu haka kamfanonin ƙera makamai sama da dubu biyu daga ƙasashe aƙallla 60 ke halarta a arewacin birnin Paris, babban birnin Faransa.
Chadi ta tabbatar da mutuwar mutane da dama sakamakon wata tashin gobara a kasar.
Shugaba Biden na Amurka ya amince da bawa ma’aurata ‘yan ci rani takardar izinin zama ta dindindin.
Euro: Portugal ta sami nasara akan Czechia da ci 2:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj