Ta’addanci! ‘Yan bindiga sun harbe mutane 20 tare da jikkata wasu da dama a wajen Mauludi

📸Katsina Daily

Wani mazaunin garin ya ce yan bindigar sun kewaye wurin da ake Mauludin da harbin bindaga da wajen misalin karfe 11:5pm na daran ranar Lahadi.

Alfijir Labarai ta rawaito ƴan bindiga sun kewaye inda ake tsaka da gudanar da bikin Mauludi a garin Kusa, dake cikin karamar hukumar Musawa nan jihar Katsina, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Haka kuma wadanda suka jikkata da harbin bindaga yayin harin sun kai mutum 17 maza da mata da kananan yara, inda aka wuce da wasu asibitin ƙashi dake Katsina, wasu kuma aka yi da su General Hospital dake cikin garin Musawa.

Wani mazaunin garin ya ce yan bindigar sun kewaye wurin da ake Mauludin da harbin bindaga da wajen misalin karfe 11:5pm na daran ranar Lahadi, inda sukai ta harbin yan mauludin har lokacin da Allah Ya kawo jami’an tsaro sannan suka gudu zuwa cikin dajinsu

Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan kawo hari sun harbi mutum 18, daga cikinsu biyu sun rasu bayan an kai su zuwa asibiti.

Ya ce yanzun haka sun dukufa kan bincike tare da ganin sun cafke duk masu hannu a cikin wannan harin don gurfanar da su a gaban kotu.

Katsina Daily News

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *