Mazauna yankin sun bayyana cewa cewa ’yan kungiyar asirin sun yi musayar wuta da DPOn da jami’ansa.
Alfijir Labarai ta rawaito Wasu ’yan kungiyar asiri sun fille kan wani Babban DPO Mai Kula da yankin Ahoada da da ke Karamar Hukumar Ahoada ta Jihar Ribas.
’Yan kungiyar asirin sun fille kan DPO mai suna CSP Bako Amgbasim ne a lokacin da ya jagoranci ’yan sanda suka kai samame maboyar ’yan wata kungiyar asisi mai suna Icelanders.
Mazauna yankin sun bayyana cewa cewa ’yan kungiyar asirin sun yi musayar wuta da DPOn da jami’ansa.
Majayarmu ta ce ana cikin haka ne harsasan ’yan sandan suka kare, shi ne ’yan kungiyar suka yi musu kwanton bauna suka cafke su, suka kakkashe.
A wani bidiyo da wakilinmu ya gani, an nuna gangar jikin marigayin, inda aka ji muryar wasu na caccakar sa bisa karfin halin DPO Bako Ambasim na yin fada da ’yan kungiyar asiri ta Icelanders.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ta tababar da faruwar lamarin.
Karamar Hukumar Ahoada ta Jihar Ribas ta yi kaurin suna wajen ayyukan kungiyoyin masu gaba da juna.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb