Rundunar sojin ƙasa da haɗin gwiwar jami’an DSS sun daƙile shirin ƴan BH na kai wasu hare-hare a Birnin Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito Jami’an sun kama waɗan ake zargin a Ƙaramar Hukumar Gezawa yayin da suke shirin aiwatar da nufinsu a sassan Kano.
Mai magana da yawun rundunar sojin Brig. Gen. Nwachuku ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu.
Jami’an tsaron sun ƙwato makamai da dama daga wajen ƴan ta’addar.
“Jami’an tsaron hadin gwiwa wadanda suka hadar da sojoji da jami’an tsaron farin kaya wato DSS sun samu nasarar gudanar da aikin dakile hare-haren ta’addancin ne a yau juma’a, a karamar hukumar Gezawa a Kano”.
Kakakin rundunar ya bada tabbacin jami’an rundunar zasu cigaba da aiki ba dare ba rana don tabbatar da kare dukiyoyi da rayukan al’ummar jihar kano da kasa baki daya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp