Alfijr ta rawaito Shahararrun yan film din nan wato Ty Shaba da Shariff Aminu Ahlan wadanda suke shugabantar kungiyar A.A
Zaura Celebrities Forum da suka karrama Zaura din yau wajan wata bakwai ko takwas sun musu sama da fadi da hafsin da aka basu dan raba musu.
Dama Hausawa na cewar rana bata karya, sai dai uwar diya taji kunya, wasu kuma su ce komai ni san dare gari zai waye.
Idan za ku iya tunawa a karshan shekarar da ta gabata ne wasu yan kungiyar Kannywood suke zargin shugabannin sun cinye kudaden da ɗan takarar Majalisar Dattijai a Kano ta tsakiya A.A. Zaura din yai musu alkawari a lokacin da suka karramashi.
A lokacin Shugabannin sun Musanta zargin, a in da wasu suke ganin shifcin gizo ne, dan ba yadda Zaura din zai alkawari a idon duniya ace fiye da wata shida bai cika ba a karamcinsa.
Wani binciken da jaridar Alfijr ta yiwo tabbas an bar baya da kura.
Wasu manyan masana’antar wadanda suka bukaci a saya sunansu sun tabbatar wa Alfijr cewar a watan Junairun sabuwar shekarar da muke ciki, A.A. Zaura din ya basu makudan kudi da manyan motoci da zasu dunga yi masa yawan campaign dasu.
Haka kuma ya basu makudan kudade lokacin da dan takarar shugabancin kasa Asiwaju Tinubu ya kawo ziyara, amma suka yi sama da fadi dasu, suka barsu da manyan riguna da huluna.
Hakan tasa suka ki zuwa su yiwa gwannin nasu rakiya a lokacin taron.
Kuma har zuwa yanzu sun tabbatar Ahlan din da Shaba basuce musu ga sisi ba.
A yanzu sunci alwashin fara gayawa duniya Kauracewa goyan bayansu ga tafiyar A.A Zaura din.
Hakazalika sun yi Kira da dan takarar da yai gaggawar daukar mataki akan Shugabannin wanda suke neman goga masa bakin jini a masana’antar Kannywood din.
Mun nemi jin tabakin wadanda ake zargin amma Ty Shaba bamu samu wayarsa ba, a inda Shariff Ahlan da muka samu yai magana cikin fushi inda yace suyi kararsu mana tunda akwai hukunci.
A yanzu haka mun zura ido muga yadda zata kare.
Shin gaske ne, ko kuma kotu zata rabasu ?
Karin bayani na nan tafe…
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Bestseller ingantacciyar kafar samun sahihan labarai
Alfijir ingantacciyar kafar samun sahihan labarai da dumiduminsu
Muna godiya