DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
NTA ZARIA
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
Tabbas abu ne mara dadi Rasuwa irin ta dattijai na kwarai wadanda su kayi shura rayuwa musamman wadanda suka gudanar da rayuwar su wajen hidimtawa al’ummar su, suka gudanar da siyasa tsaftatacciya suka kuma yi aiki tukuru bisa gaskiya, adalci, rikon amana da kuma gujewa tara abin duniya duk da irin manyan mukaman da suka rike.
Marigayi Sanata Ahmed Zakari Birniwa na daya daga cikin ire iren wadannan bayin Allah kasancewarsa gogaggen dan siyasa wanda ya sha gwagwarmayar tabbatar da gaskiya, adalci da kuma wakilcin al’umma nagari.
An haifi Sanata Ahmed Birniwa shekarar 1939, a garin Birniwa da ke masarautar, Kuma Gundumar Hadejia a tsohuwar Jihar Kano (Yanzu kuma Jihar Jigawa).
Ya fara karatun addini a gaban mahaifinsa wanda Alkali ne a wancan lokacin, sai kuma makarantar Allo. Ya fara karatun Elementary a karamar Makarantar Firamare ta Birniwa a shekarar 1947 zuwa 1950 sai kuma Babbar firamare ta Hadejia a shekarar 1950 zuwa 1953.
Daga nan ya wuce Makarantar Midil(Provincial Secondary School Kano) Wato Rumfa College Kano daga 1954 zuwa 1959.
Ya wuce zuwa Makarantar Koyon aikin likitan Hakori ta Gwamnatin Najeriya dake Ikko a lokacin Sir Ahmadu Bello yana Firimiyan Jihar Arewa.
Ya zama gogaggen Likitan Hakori a jihar Kano kafin ya tsunduma harkar siyasa a shekarar 1975 inda ya rike shugaban Karamar hukumar Hadejia a shekarar 1977 zuwa 1979.
Ya shiga zaben Sanata a Jam’iyyar PRP karkashin jagorancin Mallam Aminu Kano ya kuma samu Nasara da kuri’u masu rinjaye a zaben shekarar 1979. Ya zama Sanata a Jamhuriya ta biyu inda ya wakilci Yankin Kano ta Arewa maso Gabas da suka hada da masarautun Hadejia, Gumel da Kazaure.
Sanata Ahmed Birniwa mutum ne jajirtacce wanda yasan makamar aiki, sannan kuma ga iya magana musamman a zamansa a Majalisar Dattijai a lokacin Shugaban kasa Shehu Shagari wanda yakan samu girmamawa daga takwarorinsa sanatoci a duk lokacin da ya kawo kudiri a zauren majalisar Dattijai dake Ikko.
Dan gwagwarmayar kawo cigaban al’umma wanda yayi fice wajen kudirin samar da sabuwar jihar Hadejia tun a shekarar 1988 inda ya taba zama shugaban masu kokarin tabbatar da kudirin samun Jihar Hadejia.
Marigayi Sanata Ahmed Zakari Birniwa ya zamo uba a bangaren cigaban al’ummar Kano da Jigawa wanda har zuwa rasuwarsa jigo ne a gamayyar Dattijan Jihar Jigawa (Jigawa State Elders Forum).
Hakazalika kusa ne cikin wadanda suka assasa kungiyar Tsoffin Dalibai ta kwalejin Rumfa dake Kano (wato Rumfa Old Boys Association RUMFOBA).
Mutum ne mai Tsantseni da gudun duniya duba da irin yadda ya gudanar da rayuwar sa cikin sauki, ba tare da handama da babakere irin na wasu yan siyasar da suka rike mukamai a kasa ba.
Dattijo ne wanda al’umma ke matukar amfana dashi wajen bada shawarwari nagari da nufin cigaban al’umma mai dorewa.
Ya rasu yau Litinin 26 ga Febwairu 2024 bayan gajeruwar rashin lafiya. Dattijon arziki mai shekaru 85 (1939 – 2024) ya bar mata biyu ‘ya’ya 20 da jikoki da dama.
Allah ya gafartawa Baba Sanata Ahmed Birniwa yasa Aljannah makoma, mu kuma ya kyautata namu zuwan Ameen.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
Mashaa Allah
Allah yaji qan maza jiya yayi masu afuwa