Ta addanci! Yan Bindiga Sun Kashe Mai Unguwa Da Mutane 7 Sun Kuma Kone Motoci 8 Da Gidaje Da Dama

FB IMG 1708414552469

Cikin wadanda suka kashe har da mai unguwa Haruna Wakili da kuma wani yaro da suka yi ma mummunan kisa ta hanyar ƙone shi kurmus a cikin ɗaki

Alfijir labarai ta rawaito ta’addancin da yan bindiga suka yi daran jiya a ƙauyen Yan-nasarawa, ƙaramar hukumar Faskari, munin ya yi yawa, yayin da suka kashe aƙalla mutum 6 nan take ciki har da kone yaro daya kurmus a cikin daki, da kuma hallaka mai unguwar garin

A mummunan harin da yan bindiga suka kai daran jiya Litinin wayewar garin yau Talata, a garin Yan-nasarawa dake cikin karamar hukumar Faskari, bisa rahotannin farko da muka samu daga waɗanda lamarin ya rutsa da su, yan cikin garin sun tabbatar da kashe masu aƙalla mutum shida ciki har da mai unguwar garin Malam Haruna Wakili.

Auwal Liman Hassan Nasarawa, daya daga cikin mazauna garin ya bayyana mana cewa, cikin wadanda yan bindigar suka kashe har da wani karamin yaro da suka ƙone shi kurmus ta hanyar banka masa wuta a cikin dakin da yake ciki yana barci.

“Sun kuma harbar mana mutum takwas, sannan sun kone motoci takwas da muka kirga cikin daran bayan sun gama ta’addancin sun gudu.

“Cikin wadanda suka kashe har da mai unguwa Haruna Wakili da kuma wani yaro da suka yi ma mummunan kisa ta hanyar ƙone shi kurmus a cikin ɗaki” Inji Auwal Yan-nasarawa.

Shima a nasa karin bayanin Abdullahi Adamu Nasarawa da abin ya afku a gabansa da suka sha da kyar ta hanyar shigewa cikin daji bisa dutse, ya ce cikin wadanda suka kashe har da wani magidanci da suka yi ma yankan rago, “Wallahi a yanzun ma ba mu iya gane wadanda suka kwasa suka yi cikin daji da su, sai hari ya ida wayewa za a ida tabbatar da ko mutum nawa ne ba a gan shi ba dake hannunsu” Inji Abdullahi Nasarawa

Haka kuma sun tabbatar da cewa yan bindigar sun kone masu aƙalla shagunan sayar da kayan masarufi goma, tare da gidaje da dama

FB IMG 1708414547627
📸 Katsina Daily News
FB IMG 1708414562470

📸 Katsina Daily News

 Katsina Daily News
📸

Katsina Daily News

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *