Sun Yi Amai Sun Lashe! Hukumar Alhazan Najeriya Ta Sanar Da Ƙarin farashin Hajin Bana


Alfijr ta rawaito Hukumar Alhazan Najeriya tayi amai ta lashe bayan da ta bayyana cewar ba za ta yi karin ko ranyo ba to yanzu zance dai ya sha bambam, zanen da nake muku yanzu dai hukumar ta bayyana  karin Dala 100 ga duk wani maniyyacin da zai gabatar da aikin hajin wannan shekara.


anarwar ta tace sabon matakin ya biyo bayan rikicin da ake ci gaba da yi a kasar Sudan, abinda ya tilastawa jiragen da za suyi jigilar maniyata kaucewa bi ta sararin samaniyar kasar da kuma tsawaita tafiyarsu.

Ta Bayyana karin da aka samu ya kai na Dala 250 akan kowanne maniyacci.

Sai dai hukumar ta bayyana cewar  tayi nasarar shawo kan kamfanonin jigilar maniyatan yin ragi, yayin da za’a ragewa kowanne maniyaci kudin alawus da za’a bashi daga Dala 800 zuwa Dala 700.

Akalla maniyata dubu 75 ake saran su sauke farali daga Najeriya a Hajjin bana kamar yadda hukumar ta bayyana.

RFI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *