Daga Aminu Bala Madobi
Kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka sun bi sahun sauran mutane wajen nuna damuwa na tsare Bazoum din.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban “ya gana da likitansa a ranar Asabar, wani memba na tawagarsa ya shaida wa kafar AFP cewa likitan ya kuma kawowa Bazoum da matarsa da dansa da ake tsare da su abinci mai rai da lafiya.
Majiyar ta kara da cewa “Yana cikin koshin lafiya, idan aka yi la’akari da halin da ake ciki.”
Tun bayan da sojoji suka karbe mulki tare da kama su a ranar 26 ga watan Yuli, ake ci gaba da nuna fargaba kan yanayin lafiya da tsare Bazoum da matarsa da dansa mai shekaru 20 a duniya.
Kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka sun bi sahun sauran mutane wajen nuna damuwa na tsare Bazoum din.
Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce yanayin tsare Bazoum da aka rawaito “zai iya zama rashin mutunta dan adam, wanda ya saba wa dokokin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa”.
Babban jami’in diflomasiyyar Amurka Antony Blinken ya ce “ya ji takaici” da kin sakin dangin Bazoum da sojoji suka yi.
Kafar labaran CNN ta rawaito a makon da ya gabata cewa Bazoum na keɓe tare da tilasta wa waɗanda suka hambarar da shi cin busasshiyar shinkafa da taliya.
A halin da ake ciki kuma, yar shugaban kasar wadda ta tafi hutu a kasar Faransa lokacin da aka tsare danginta, ta ce tana tuntubar mahaifinta da mahaifiyarta da kuma dan uwanta a kowace rana ta wayar salula, wadanda ta ce suna rayuwa ba tare da tsaftataccen ruwan sha ba, kuma suna dogaro da shinkafa da taliya, ko da yake abincin ba mai dadi ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Allah ya kyauta.