Sojoji Sun Kwato Mutane 9 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Tare Da Kwato Kudin Fansa A Zamfara

Sojoji sun samu nasarar karbo mutane 9 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su tare da ƙwato kuɗaɗe da makamai a ƙauyen Gadazaima na jahar Zamfara.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan artabu da ƴan bindigar, inda sojojin suka samu nasarar kashe ‘yan bindiga 10 tare da raunata wasu da-dama a lokacin gumurzun.

Haka zalika, Sojojin sun kama mutane biyu daga cikin ‘yan bindigar, tare da Bindigogi shidda kirar AK-47, Bindiga 1 kirar 1PKT da kuma Magazine 5. Sauran sune bulet 7.62MM mai rawun 20, wayoyin hannu 3, Fanel din Sola 2, Keken ɗinki da Naira Miliyan 2,410,000.

A rahoton da “Rariya ta samu ƴan bindigar sun kashe wata mace wadda tana daga cikin mutane tara da sojojin suka kuɓutar daga hannun ƴan ta’addan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

2 Replies to “Sojoji Sun Kwato Mutane 9 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Tare Da Kwato Kudin Fansa A Zamfara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *