
Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Kaduna, ta ce farmakin da sojojin saman Najeriya suka kai a yankin karamar hukumar Birnin Gawri da ke jihar, sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da suka tsere.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kaduna.
Aruwan ya ce da misalin karfe 9:44 na safe ne ma’aikatar ta samu kiran ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Sabon Layi da ke karamar hukumar Birnin Gwari.
“An tabbatar da cewa ‘yan bindigar na harbi, suna satar shanu, suna wawushe dukiyoyi da kuma aikata wasu munanan laifuka, lamarin da ya sanya mazauna garin suka yi kaca-kaca da su domin tsira da rayukansu.”
A cewarsa, an tuntubi rundunar sojin sama na Operation Whirl Punch domin daukar mataki, kuma rundunar ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba.
“Duk da haka, kimanin kilomita hudu daga Arewacin kauyen Sabon Layi, an hangi ‘yan bindigar suna guduwa domin neman mafaka daga jirgin.
Kwamishinan ya bayyana cewa ba a sake samun wani motsi ba bayan harin ta sama.
“Jirgin ya ci gaba da kasancewarsa a sama kafin ya janye.
“Yayin da gwamnati ke jiran rahoton a hukumance kan harin farko da aka kai kauyen Sabon Layi, Gwamna Nasir El-Rufai ya yabawa rundunar sojin sama bisa matakin da ta dauka na gaggawa, sannan ya mika godiyarsa kan yadda aka kashe ‘yan bindigar da suka tsere.” Inji Aruwan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ