Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yakin da Isra’ila take gwabzawa da Falasdinawa a Zirin Gaza.
Alfijir Labarai ta rawaito ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana a taron da ake gudanarwa a ƙasar Saudiyya da kasashen Afirka a Riyadh.
Hakazalika Shugaba Tinubu ya ba masu sha’awar zuba jari da cewa Najeriya waje ne mai albarka da ba za su yi da-na-sanu ba muddin suka shigo domin kasuwanci.
Ya kuma bukaci a ruɓanya alaka da Saudiyya domin shawo kan matsalar Boko Haram da ISWAP da ma ta sauran kungiyoyi masu tsauraran ra’ayoyi da suka addabi yankin Tafkin Chadi da na Sahel.
“Najeriya da Saudiyya sun jima suna hulda da juna a matakai daban-daban.
Shekaru 60 da suka gabata, alakarmu ta faɗaɗa, sabanin abinda bai wuce aikin Hajji ba a baya.
“Abin farin cikin yanzu shi ne ƙaruwar ’yan kasarmu a ɓangarorin lafiya da kwallon kafa da dai sauransu.
“Najeriya, kamar Saudiyya, tana aikin fadada tattalin arzikinta don ya tashi daga mai dogaro da man fetur zalla domin a samu ci gaba. Gwamnatina ta dauki wani mataki mai matukar wahala na cire kudaden ta ake tabargazarsu wajen biyan tallafin man fetur da kuma daidaita farashin canjin kudaden kasashen waje da sauran manufofin da za su dada saukaka kasuwanci a Najeriya,” in ji sanarwar.
Tinubu ya kuma gode wa gwamnatin Saudiyya saboda bayar da ayyukan jinkai a Najeriya ta hannun Gidauniyar Bayar da Tallafi ta Sarki Salman.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp