Shugaban karamar hukumar ya yanke jiki ya faɗi ya rasu kwana daya kafin zabe

IMG 20231110 WA0012

Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Hon. Mohammed Dan Asabe Muhammad, ya rasu.

Alfijir Labarai ta rawaito an tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 4:30 na safe a wani asibiti da ke Lokoja babban birnin jihar.

An garzaya da Muhammed asibiti bayan da ya yanke jiki ya faɗi a gidansa.

An ce ya halasci tarurrukan siyasa ne na shirye-shiryen zaben gwamnan da za a yi a gobe Asabar.

Wata majiya daga dangin mamacin ta ce an garzaya da shi asibitin Shifa, Lokoja, jim kadan bayan ya faɗi a gidan da yammacin ranar Alhamis.

“Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa a asibiti da misalin karfe 4:30 na safiyar ranar Juma’a,” in ji wani dangin da ya nemi a sakaya sunansa.

Marigayin ya fito ne daga mazabar B dake yankin Lokoja.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Shugaban karamar hukumar ya yanke jiki ya faɗi ya rasu kwana daya kafin zabe”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *