Shugaban Kamfanin Jirgin Ƙasa Ya Tsallake Rijiya Bayan An Kashe Ɗan Sandansa

Alfijr ta rawaito Manajan Daraktan Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya, Thimothy Zalanga, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bude wa ayarin motocinsa wuta, suka kashe dan sanda da ke tsaron lafiyarsa.

Mista Zalanga ya ce shi da sauran mutane da ke motarsa sun tsallake rijiya da baya ne bayan ’yan bindigar sun bude musu wuta dab da shigarsu garin Kaduna, bayan dawowarsu daga Abuja.

“An harbe Sufeto Aminu Muhammad da ke zaune a kujerar gaba har lahira, ni da direban da Sajan Allen Moses kuma mun tsallake rijiya da baya,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Abin ya faru ne a lokacin da Sufeto Aminu yake tsaka da waya da iyalansa cewa ya kusa zuwa gida.”

A ziyarar ta’aziyyarsa ga Ofishin ’Yan Sanda na unguwar Donwn Quarters da ke Kaduna, Zalanga ya ce ’yan bindigar sun kai musu harin ne da misalin karfe 9 na dare ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, 2022.

Ya yi addu’ar samun rahama ga Sufeto Aminu Muhammad, tare da alkawarin cewa kamfanin zai ci gaba da tallafa wa iayalansa.

Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya wani rukuni ne karkashin Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC).

“Muna tuntubar iyalan marigayin, duk da cewa mun san babu wani abin da za mu iya yi da zai maye gurbinsa, amma za mu yi iya bakin kokarinmu wajen tallafa musu,” in ji shi.

Daga nan ya wa Sajan Moses da suka tsallake rijiya da baya tare tallafin kudi, ya kuma ba wa caji ofis din gudummawar babur, “domin saukaka muku aiki, saboda na samu bayanin yadda kuke fama a duk lokacin da kuka samu kiran gaggawa daga al’umma.

“Muna fata a farkon shekara mai zuwa mu ba da gudmmawar mota.”

A jawabinsa, DPO na Down Quarters, SP, Victor Allahmagani, ya yaba wa shugaban kamfanin jiragen kasan bisa ziyarar ta’aziyyar da kuma gudummawar, wadda ya ce za ta taimaka wajen saukaka musu ayyukansu.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *