Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Misis Adedayo Benjamins-Laniyi a matsayin babbar sakatariyar harkokin mata ta gwamnatin tarayya (FCTA).
Alfijir Labarai ta rawaito Mista Anthony Ogunleye, Daraktan yada labarai na ofishin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.
Ogunleye ya ce Benjamins-Laniyi zai taka muhimmiyar rawa a kudurin FCTA na inganta walwala da karfafawa mata da yara a babban birnin tarayya.
Ya bayyana fatansa na cewa nadin nata zai kara karfafa kwarin guiwar gudanarwa karkashin jagorancin Wike da karamar ministar kasa, Dr. Mariya Mahmoud.
Ogunleye ya kara da cewa, an nada Benjamins-Laniyi, wacce aka haifa a shekarar 1965 a Ogun, an nada ta ne saboda cancantarta da sadaukar da kai ga aikin gwamnati.
“Tare da fiye da shekaru 35 na kwarewa a matsayin mai ba da shawara kan sadarwa, ‘yar kasuwa na zamantakewa, mai ba da shawara na kasa da kasa, da kuma muhalli, Misis Benjamins-Laniyi ana sa ran za ta kawo ci gaba mai yawa ga sabon aikinta.
“Ta halarci Kwalejin Queens da ke Legas, don karatun sakandare, kuma ta yi karatun Turanci a Jami’ar Ibadan a shekarar 1989.
“Sha’awarta ga al’amuran zamantakewa, musamman wadanda suka shafi mata da yara, ya bayyana a cikin gagarumin aikinta.
“Ta kuma nuna jajircewarta na shiga harkokin siyasar mata ta hanyar neman kujerar sanata a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2022,” inji shi.
A cewarsa, zurfin fahimtar da ta yi game da yanayin siyasa da kuma iya tafiyar da kalubalen siyasa masu sarkakiya ba shakka za su taimaka wajen ci gaban yancin mata da walwala a babban birnin tarayya Abuja.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo