Shugaba Tinubu Ya Sake Bayyana Nadin Sabbin Mataimaka Na Musamman

Shugaba Bola Tinubu ya nada Kingsley Stanley Nkwocha, tsohon Manaja kuma Editan Jaridar Leadership Daily, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (SSA) kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa a Fadar Shugaban Kasa.

Alfijir Labarai ta rawaito an nada Nkwocha ne tare da wasu da dama da za su yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Tinubu ya kuma nada Tope Fasua, babban jami’in gudanarwa (Shugaba) na Global Analytics Consulting, a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki a ofishin VP.

A cikin jerin sunayen, wasu da aka nada a ofishin mataimakin shugaban kasa sun hada da :-

Sadiq S Jambo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki,

Dr. Muhammad Bulama, a matsayin
babban mataimaki na musamman,

Mahmud Muhammad a matsayin mataimakin na cikin gida arewa-maso-gabas

Ahmed Ningi a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na zamani. da Gudanar da Gaggawa.

“Shugaba Tinubu ya nada sabbin mataimaka a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Stanley Nkwocha SSA Media (VP Office);

Tope Kolade Fasua, Mashawarci na Musamman Tattalin Arziki (VP Office);

Sadiq S Jambo SA Economy (VP Office).

“Dr. Muhammad Bulama SSA Special Duty (VP Office);

Mahmud Muhammad Mai Taimakawa Na Cikin Gida Arewa-maso-Gabas (VP Office);

Ahmed Ningi, SSA Digital Media da Gudanar da gaggawa (VP Office);

Musa Amshi Muhammad Al-Amin, SSA Special Duties (VP Office);

Emmanuella Eduozor a matsayin SA Multimedia Content Production,”

Gimba Kakanda, marubuci kuma manazarci harkokin jama’a, an kuma nada shi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman, Bincike da Nazari (VP Office).

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *