Alfijir Labarai ta rawaito shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa
Wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar kasar ya fitar ranar Laraba ta ce an dakatar da Abdulrasheed Bawa domin samun damar gudanar da bincike a kan ofishinsa.
“Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Mr. AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) domin samun damar gudanar da binciken da ya dace kan ayyukan da ya yi lokacin da yake rike da ofishinsa,” a cewar sanarwar da Willie Bassey, daraktan watsa labarai na Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ