
Alfijr ta rawaito Shugaba Buhari zai halarci taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra babban birnin ƙasar Ghana.
Hakan na kunshe ne cikin wani saƙo da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce shugaban zai bar Najeriya ranar Talata 25 ga watan Afrilu domin halartar taron, wanda shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranta.
Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.
Yayin halartar taron, shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin ƙasashen wajen ƙasar Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno mai ritaya, da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami’an gwamnati.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ