Shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Dakta Jamila Bio Ibrahim a matsayin ministan kula da harkokin Matasa.
Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale da ya fitar a ranar Lahadi, shugaban ya kuma amince da nadin Ayodele Olawande a matsayin karamin ministan harkokin matasa.

Dukkansu, za su halarci Majalisar Dattawan Nijeriya domin tantance wa.
Dakta Jamila Bio Ibrahim matashiyar likita ce wacce a baya-bayan nan ta kasance shugabar kungiyar Mata ta ‘Progressive Young Women Forum’ (PYWF).
Ta taba yin aiki a matsayin babbar mai taimaka wa gwamnan jihar Kwara kan manufofin cigaba mai daurewa (SDGs)

Shi kuma, Ayodele Olawande kwararren masani ne a bangaren cigaban al’umma kuma shugaban matasa ne a jam’iyyar APC.
Aikin da ya yi a baya-bayan nan kafin wannan nadin shi ne ya kasance babban mashawarci ga shugaban kasa kan kirkire-kirkiren zamani daga shekarar 2019 zuwa 2023.
A kan hakan, shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci wadanda aka nadan da su yi amfani da azamarsu, kokarinsu, hikimarsu, dabararsu wajen kyautata al’amuran Matasan Nijeriya yayin da suke gudanar da ayyukansu.
The Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb