SERAP ta kai karar Shugaban Majalisar Dattawan Da Kakakin Majalisar Wakilai kan Bacewar’ N4.1bn
Best Seller Channel
Best Seller Channel
SERAP ta kai karar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, a kan “ gazawar da suka yi wajen yin bincike, da kuma mikawa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da suka dace da zarge-zargen bacewar N4.1bn na kudaden al’umma da aka ware wa Majalisar
Kudaden, an karkatar da su ko kuma an sace su.
Punch ta rawaito wannan kara ta biyo bayan fitar da rahoton da aka tantance na shekara ta 2016 wanda Audita- Janar na tarayya ya nuna damuwa game da zargin karkatar da dukiyar jama’a tare da neman a dawo da duk wasu kudade da suka bata”
Best Seller Channel
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1609/2021 da ta shigar a babban kotun tarayya dake Abuja, SERAP na neman , ” Umarni na mandamus ya umurnin tare da tilasta Dr Lawan da Mista Gbajabiamila su gudanar da ayyukansu na sa ido kan tsarin mulkin kasar don gaggauta bincike kan zargin da aka yi na cewa N4.1bn na kasafin kudin majalisar dokokin kasa ya bace.
A cikin karar, SERAP na jayayya cewa “Majalisar dokokin kasar tana da ayyukan doka da tsarin mulki don hana cin hanci da rashawa, tare da tabbatar gaskiya da rikon amana a cikin tafiyar da dukiyar al’umma.
“Majalisar dokokin kasa za ta iya yin aikinta na yaki da cin hanci da rashawa kawai idan ta iya nuna kyakkyawan jagoranci don bincikar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ke tattare da majalisar.
Best Seller Channel
SERAP tana kuma jayayya cewa, “tsarin gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da dukiyar al’umma ya na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ci gaba da jin dadin jama’a tare da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum, da kuma samar da kyakkyawan shugabanci da gudanar da mulki cikin tsari.
SERAP dai na jayayya da cewa, “Rashin binciken da Majalisar Dokoki ta kasa ta yi cikin gaggawa, da kuma duba ga hukumomin da suka dace na yaki da cin hanci da rashawa da zarge-zargen da aka rubuta a cikin rahoton da aka tantance na shekara ta 2016, wani babban cin zarafi ne na sa ido da ayyukan da jama’a da suka dora musu
Best Seller Channel
Majalisar dokokin kasar ba ta da wani dalili a shari’a na kin binciki zargin da ofishin Odita-Janar na Tarayya ya rubuta.” Lauyoyinta Kolawole Oluwadare da Kehinde Oyewumi ne suka shigar da karar a madadin SERAP.