
Jam’iyyar NNPP ce ke kan gaba da kuri’u sama da 100k yayin da ‘yan jihar Kano ke jiran sakamakon karamar hukumar Dala ta Kano, wanda shine zai kawo kammala tattara zaben gwamnan Kano a 2023.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tattara sakamakon wasu kananan hukumomi 43, inda jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ke jagorantar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuri’u 102,983.
Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 964,808, Nasir Gawuna na APC ya samu kuri’u 861,825.

Tuni dai magoya bayan jam’iyyar ke ta murna da abin da suke ganin alama ce ta nasara amma har yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa bata kammala aikin ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇