Satar da garkuwa da mutane yanzu muka fara -In Ji Ɗan Bindiga Dogo Giɗe

FB IMG 1696410352896

Ina so in gayawa duniya, su karya suke yi, ni bana son sulhun wallahi bani son sulhu, wallahi bana son zaman lafiya.

Alfijir Labarai ta rawaito babban dan bindiga nan da ke zaune a yankin jihar Neja kefen kontagora ya fitar da wani sabon sako zuwa ga al’umma najeriya, cikin wani faifan sautin murya da yake a shafukan sada zumunta inda Bello Mu azu ya dora a shafinsa.

Idan baku manta kwanan baya anga bidiyo da ya fitar wanda yaransa suke ikirarin sune suka tarwatsa jirgin sojoji da yayi sanadiyyar mutuwar hazikin sojojin Najeriya.

“Satar mutane yanzu ma muka fara saboda akwai dalili saboda satan da akayi yanzu ne ma zamu yi shi, kuma ina son wannan sako ya ishe kunnen kowa dan Allah.

Yanzu tsakanina da Allah yanzu in kaji nayi satar mutum goma na rantse da Allah a gabar wannan labarin mutum bakwai 7 zan kashe, mutum uku zasu koma, inaso in gayawa duniya, su karya suke yi, ni bana son sulhun wallahi bani son sulhu, wallahi bana son zaman lafiya.

Dogo giɗe ya kara da cewa:

“Ni wallahi duk mai neman zama lafiya baida albarka, ni na yarda zamana lafiya naci na sha da iyalina cikin daji, in sha Allahu ni dai da gari sai dai in bayan rayuwata na hakura da gari.

Ni daji yanzu ya zamu uwata ya zamu ubana, cikin daji nan ne zan ga wuya in boye in samu daɗi na in yi zama na, ina rokon Allah ya tayani zamana a cikin dajin nan.

Bani buƙata gari ko miliyan dubu gwamnati zata bani dan in daina ta’addanci wallahi na yafe, ranar ta same ni bana son ta barni da rayuwata.”- inji dan bindiga.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *