Sarkin Kano Ya Yabawa Hukumar Custom Bisa Samun Fahimtar Juna Da Yan Kasuwa

IMG 20240308 WA0211

Mai martaba sarkin kano Alhaji Amunu Ado Bayero ya nuna gansuwarsa bisa yanda aka samu fahimtar juna tsakanin yan kasuwa da jami’an hukumar fasa kauri ta kasa wato Custom wajen sakar musu mara ba tare da shiga kasuwanni ana kwashe musu kaya ba.

Alfijir labarai ta rawaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakoncin shugaban hukumar fasa kauri ta kasa Bashir Adewale Adeniyi a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero wanda yace abaya sun sha karbar korafe korafe na yan kasuwa bisa yanda jami’an hukumar custom suke shiga kasuwanni su kwashe musu kaya wanda a yanzu abun bahaka yake ba.

Haka zalika mai martaba sarkin ya bukaci babban kwantirolan na kasa idan zasu raba kayan abinci dasu duba mabukata wajen raba musu kayan tare da basu goyon baya tare da hadin Kan masarautar kano baki daya.

A nasa jawabin babban shugaban hukumar hana fasa kauri ta kasa wato custom Bashir Adewale Adeniyi yace sunzo fada ne domin neman tabarrakin sarki da shawarwari akan aiyukan su na hukumar custom.

Shugaban hukumar hana fasa kaurin ya samu rakiyar shugabn hukumar custom shiyar kano da Jigawa Dauda China da kuma manyan jami’an hukumar ta custom.

Kamar yadda Abubakar Balarabe Kofar Na’isa Baban Sakataren yada labarai na Masarautar Kano ya saka hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *