A madadin Lisanul Faidha Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A) Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero na gayyatar Yan uwa Musulmi Musamman Yan Darikar Tijjaniyya zuwa taron zikirin Juma’a da yiwa kasa addu’a na Shekara a karkashin Jagorancin Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A).
Za’a gudanar da wannan taro ne a ranar Juma’a 28 ga watan Zul Hajj Shekara ta 1445 bayan hijihar Annabi Muhammadu SAW wadda tayi dai dai da 5 ga watan yuli Shekara ta 2024 milidiyya da karfe 4 na yamma a Kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero dake Nassarawa a birnin Kano.
Shugaban taro Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, bakon alfarma Mai girma Shugaban Kasar Najeriyya Alhaji Ahmed Bola Tinubu, Babban bako na Musamman Lisanul Faidha Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A).
Ana saran halartar Manyan shehunnai da mukaddamai da murudai daga sassa daban daban na ciki da wajen Kasar nan.
Sanarwa daga Khadimul Faidha Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi.

Allah ya bada ikon zuwa Ameeeeen.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj