Sarki Kano Aminu Ado Bayero Ya Baiwa Hakimai Umarni Shirin Hawan Sallah

FB IMG 1716833360872

Mai Martaba Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci hakimai da su shigo Kano ranar asabar domin shirye-shiryen gudanar da Hawan Sallah babba.

Alfijir labarai ta ruwaito  hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ya sanyawa hannu kuma aka turawa hakimai.

Sanarwar ta umarci hakimai da su tabbata sun Isa fadar sarkin dake gidan sarki na Nasarawa a ranar Asabar mai zuwa domin gudanar da taron da za a sanar da su yadda hawan sallar zai kasance.

Takardar mai dauke da kwanan wata 10 ga watan yuni 2024, Wanda ya yi dai-dai da 4 ga watan zul-hijja 1445 bayan hijira, tace tun masarautar Kano ta sanar da shugabannin kananan hukumomi yadda zasu taimakawa hakiman don gudanar da bikin sallah babbar cikin lumana.

IMG 20240611 WA0166
Hawan Sallah

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *