Sarki Aminu Ado Ya Magantu Akan Takaddamar Sarautar Jihar

FB IMG 1709422107907

Sarki Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’ar Kano da su kwantar da hankalin su kuma su zauna lafiya a yayin da ake ci gaba da takaddama kan sarautar jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Aminu Bayero ya yi wannan kira ne yayin ganawa da shugabannin tsaro a Fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa.

Sarkin ya yaba wa shugabannin tsaro dangane da ziyarar da suka kai masa, ya kuma tabbatar da cewa nan gaba kadan gaskiya za ta yi halinta.

Ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da Najeriya baki daya, yana mai kira ga Kanawa da su zama jakadu na zaman lafiya yayin da ake dakon sakamakon shari’ar tube rawaninsa da Gwamnatin Kano ta yi.

Ya kara da cewa, suna da yakinin wadanda ragamar shari’ar da za a soma sauraro kan takaddamar sarautar Kano ke hannunsu za su yi adalci.

Screenshot 20240525 134810
Kwamatin Tsaro

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *