Sanata ya Bada Tallafin miliyan 1 da Buhu 30 na kayan abinci ga Iyalan ɗan jaridan da aka kashe

IMG 20231002 WA0118

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya bayar da gudun muwar kudi Naira miliyan daya da buhunan hatsi 30 ga iyalan marigayi Hamisu Danjibga wakilin Muryar Amurka a Zamfara.

Alfijir Labarai ta rawaito Yari wanda ya jajantawa iyalan marigayi Ɗan Jibga da ‘yan jaridar Jihar musamman wakilai masu aikewa da ruhotanni daga jihar watau (corresspondets) ya bayyana rasuwar Ɗan jibga ba karamin rashi bane Kuma gibi ne me wuyan cikewa ba ga iyalansa kadai ba har ma da kasa baki daya.

Ya ci gaba da cewa, marigayi Dan Jibga ya rasu lokacin da ake bukatar shi, ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Sanatan ya ce ya ji labarin rasuwar marigayi ne, inda ya jaddada cewa, “mutuwar tasa ta girgiza mutane da yawa musamman wadanda suka san shi”.

“Shi cikakken mutum ne kuma jajirtaccen ɗan jarida wanda za a iya tunawa da shi har abada saboda rahoton bincikensa”.

“Ina so in yi amfani da wannan damar don yin ta’aziyya ga iyalansa da takwarorinsa na ‘yan jarida, kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya kyautata makwancinsa.”

“Bisa ga halin da ake ciki, na baiwa Iyalansa kudi Naira miliyan daya da buhunan hatsi 30 a matsayin dan taimakon da nake iyi wa ga iyalansa”.

A nasa martanin, shugaban kungiyar ‘yan jarida, Alhaji Sani Haruna Dutsinma ya godewa Sanata Yari bisa wannan karimcin da ya yi masu, sannan ya yi addu’ar Allah ya saka masa da alheri ya Kara arziki da koshin lafiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *